Martanin Malam Dutsen Tanshi Ga Jafar Jafar

In ba a Manta ba kwanakin baya an yi ta samun sabani game da wasu kalamai da Malam Tanshi yayi game da ƴan Maulidi,to wannan batu dai ya tada ƙura har takai ga Sanannanen Ɗan jarida Jafar Jafar tare da sauran malaman shirin su na fashin baƙi sun ka yi zaman sharhi akan batun.

Jim Kada sai aka ga wani bidiyo yana yawo wanda malamin ya fito ya maida martani game da fashin baƙin da aka yi,ga kalamansa kamar haka;”Idan su Jafar Jafar Su Bukarti sun yi zaman fashin baƙi sai mu bar su da Allah,kasan suna zama wannan shiri mai suna sharhi,har Jafar Jafar daga cikin su yana cewa sai nayi awa guda ina maida martani akan mimbari .”

Malamin ya ƙara da cewa shi yasan malamai ne suka laƙanawa Jafar wannan kalamai,Inda malamin yayi zargin cewa Jafar ya ɗauki wannan salo ne a bakin malamai da ke yawo a kafafen sada zumunta.

Malamin ya cigaba da cewa Jafar Bai tsaya nan ba ya fito yana faɗin ”ina cewa ƴan Maulidi kafirai,wai na kafirta su,in ba tsiyar Ɗan jarida ba Me ya haɗa shi da maganar addini,su da suke fashin baƙin dimokuraɗiyya,fashin baƙin cuwa-cuwar gwamnati ,fashin baƙi a kan ECOWAS me ya shigo da su maganar addini.

Malamin ya gargaɗe su da su kiyaye shiga maganar da ta shafi addini,inda ya ƙara da cewa ƴan ayoyi da hadisai da suka iya da turanci bai kai ya kawo ba , fyace ilmin zama ƴan Ta’adda.Duk wanda ke sa baki a lamarin addini kuma baida sani to fa Dan Ta’adda ne,Har malamin yayi misali da likitoci inda yake cewa waya isa ya sa musu baki In suna bakin aikin su.

”Idan Jafar ya jahilci lamarin Shari’a kamata yayi ace Bukarti ya dawo da shi hanya saboda sanin tsarin Shari’a a matsayin sa na wanda ya karanta”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories