Boko Haram Sun Yi Sanadin Ɗaukewar Wutar Lantarki A Jihar Yobe 

Wasu da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne sun tarwatsa Tiransfomar wutar lantarki mai karfin 330KVA a jihar Yobe, lamarin da ya yi sanadin rashin wuta a jihar.

Mai baiwa Gwamna shawara Janar Ɗahiru Abdulsalam (mai ritaya), shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Damaturu.

 Ya ce ƴan ta’addan sun tarwatsa Tiransfomar ne ta hanyar fashewar bama-bamai, a yankin Kasesa a daren ranar Alhamis.

Mai Baiwa Gwamna shawara na musamman ya ce lalacewar Tiransfomar ta yi sanadiyyar rashin wuta a jihar.

 Ya ce gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar sashin 2, Operation Haɗin Kai, da kamfanin rarraba wutar lantarki na Yola, YEDC, suna kokarin ganin an shawo matsalar rashin wutan.

 NAN

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories