Ƴan Bindiga Sun Sako Shugaban Ƙaramar Hukuma A Nasarawa

Shugaban ƙaramar hukumar Akwanga Safiyanu Isah-Andaha, wanda wasu yan bindiga suka yi garkuwa da shi ranar Litinin ya shaƙi iskar ƴanci.

 DSP Ramhan Nansel, kakakin rundunar ƴan sandan jihar Nasarawan shi ne ya tabbatar da sakin shugaban tare da wasu mutane uku ga kamfanin dillancin labarai na Najeriya a jiyaTalata a garin Lafiya.

An sace shugaban ƙaramar hukumar da wasu mutane uku ne da misalin karfe 8:30 na dare a garin Ningo da ke ƙaramar hukumar Akwanga.

DSP Nansel ya bayyana cewa an sako shugaban da wasu mutane uku ne da misalin karfe 8:45 na daren ranar Talata a ƙauyen Andaha da ke Akwnaga sakamakon matsin lamba da tawagar jami’an tsaro suka yi.

Haka kuma Kakakin ya ƙara da cewa ba a biya ko sisi kuɗin fansa ba .

 Ya ce bayan samun labarin faruwar lamarin a daren ranar Litinin, kwamishinan ƴan sanda Umar Nadada, ya tura tawaga, wanda ƙoƙarinsu da jajircewar su ne ya sanya aka yi nasarar ƙwato waɗanda aka sace.

 Nansel ya ƙara da cewa wadanda aka sace a yanzu haka ana kula da lafiyar su kafin a sada su da iyalan su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories