Manoma da Ƴan kasuwa Sun Koka Kan Yadda Jami’an Tsaro Ke karɓar Haraji

Manoma da ƴan kasuwa da ke safara a kan hanyar garin Bagudo a ƙaramar hukumar Bagudu a jihar Kebbi a ranar Lahadin da ta gabata sun koka da yadda jami’an tsaro ke karɓar na goro ba ƙaƙƙautawa a shingayen da ke kan titin.

 Hanyar da ta haɗa kasar Najeriya da Jamhuriyar Benin.

 “Daga Kasuwar Tsamiya, mai safar hatsi wanda zai loda babbar mota ɗauke da buhunan masara ko gero 600 sai ya biya kudin da bai gaza Naira 600,000 ba kafin a bar shi ya isa Argungu da Birnin Kebbi.

 “Alhaji Tukur Muhammad sakataren ƙungiyar manoma da hatsi ta Amana ya bayyana cewa kowace buhun hatsi Muna biyan 1,000 waɗanda aka loda a manyan motoci, sannan kuma Naira 500 kan buhun da aka loda s babur. 

 Ya kuma danganta hauhawar farashin amfanin gona da sauran muhimman abubuwan kasuwa yana da nasaba da karɓar kuɗi da jami’ai ke yi.

“Ko da baka ɗauke da komai a Babura ɗinka sai ka biya su naira 300 kafin ka wuce zuwa kasuwa.

 “Mu ma ƴan kasa ne fa;  a matsayinmu na manoma da ƴan kasuwa, a kullum muna baƙin cikin yadda muka kasa rage farashin kayayyakin masarufi.

 “Mutane ba Sudan cewa kuma ba laifin mu bane, Wannan bani-bani da ake mana sh yake taimaka matuka wajen hauhawar farashin kayayyaki,”Alhaji Muhammad ya jaddada.

 Alhaji Muhammad Ya bukaci gwamnatin jihar da ta aiwatar da tsarin tattara kuɗaden shiga na cikin gida da kuma hana duk wani kuɗaɗen shiga ba bisa ka’ida ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories