Manyan Dalilai Da Suka Sa Shugaba Tinubu Dakatar Da Ministar Jinkai

A yau Litinin 8 ga watan Janairu 2024 ne shugaba Bola Ahmed Tinubu ta hannun mai bashi shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai Chif Ajuri Ngelale ya fitar da sanarwar dakatar da ministar jinkai Dakta Beta Edu ,Wannan Dakatarwar ya biyo bayan wasu zarge -zarge da ake tuhumar ta da shi.

Ministar dai ana tuhumar ta ne da badaƙalar naira biliyan 585.189 da ake zargin ta bada umurnin a tura su zuwa wani asusun banki.

Inda ake zargin cewa Minista Betta Edu ta rubutawa Akanta Janar ta ƙasa wasika inda ta umurce ta da sanya waɗannan kudade a cikin asusun bankin wata mata da ba’a san kowacece ita ba, lamarin da ya tayar da kura matuka.

 Sai dai jim kadan bayan fitar labarin, Akanta janar ta kasa ta bayyana cewar bata saki waɗannan kuɗaɗe ba, saboda doka sam bata bada damar sanya kuɗi a asusun wani bare ba.

 Sai dai ita kuma ministar tace dama waɗannan kuɗaɗe za a yi amfani da su ne don rabawa marasa galihu a Jihohin Akwa Ibom, Lagos, Cross River da kuma jihar Ogun .

Waɗannan batu da suka bayyana sune suka sanya cece-kuce tsakanin manyan faren hula na ƙasar inda suka umurci shugaba Tinubu da ya Tsige Betta Edu don EFCC Su sami damar gudanar da bincike game da wannan badaƙala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories