Cikin Mako Guda Tinubu Ya Aiwatar da Abinda Buhari Zai Yi A Shekara Ɗaya- Cewar Reno Omokiri

Sanannen marubuci kuma mai kwarmato bayanai a soshiyal media Reno Omokiri ya fito ya gwaɗa irin jan ƙoƙarin da shugaba Tinubu ya yi game da Tsauraran matakai da ya ɗauka akan wasu lamurra da suka taso a ƙasa Najeriya.

 Shugaba Tinubu ya dakatar da minista kan wani kuskure da ya aikata.Sannan ya gayyaci minista kan wata badaƙala da ta kunno kai.

Haka kuma shugaban ƙasar Ya rage yawan tafiye-tafiyensa ,An kori shugabannin manyan jami’an gwamnatin tarayya guda biyu saboda sakaci,Bugu da kari shugaba yi yi saurin dakatar da digirin Bogi ƴar Kwatano tare kuma da bayyana shirin gina sabuwar masana’antar karafa na kasar China a Najeriya,An ƙaddamar da tashar fasfo ta atomatik

Ya ware zunzurutun kudi har biliyan 12 ga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles da sauran kungiyoyi, Haka kuma Ya fara biyan tallafin albashi ga ma’aikatan gwamnati.

Haka kuma gwamnatin Tinubu ta fitar da Naira Biliyan 105.5 don gyaran hanyoyi 266,tare da shiga tsakani don samar da zaman lafiya a ƙasar Saliyo bayan da aka daƙile yunƙurin juyin mulki a ƙasar.

 ”Duk waɗannan nasarori shugaba Tinubu ya same Su ne cikin mako guda, Saboda haka Tinubu ya cim ma abin da Buhari zai yi kimanin shekara ɗaya kafin ya kammala. Hakan ya tabbatar da abin da na fada a lokacin yakin neman zabe, cewa duka ƴan takarar nan za su iya fin Shugaba Buhari.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories