An Tsinci Gawar Wani Mutum Rataye A Cikin Wani Kango A Kano

An tsinci Gawar wani Nuradeen Shehu a makarantar Prestige International College da ke kan titin Ɗanmusa a Gadon ƙaya ƙaramar hukumar Gwale rataye a cikin wani aji.

 Kwamishinan Ƴan sandan (CP), Hussaini Gumel, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa a safiyar ranar 28 ga watan Janairu, wani mutum mai suna Abdullahi Abdulsalam dake Rijiyar Zaki ya kawo rahoton cewa an samu Gawar Wani Almajiri mai gadi rataye a cikin wani aji.

Ya kara da cewa koda ƴan Sanda suka iso da kyar su ka ɓalle ƙofar kofar suka yi saurin yanke igiyar sannan suka garzaya da gawar zuwa babban asibitin Murtala Muhammed inda a nan ne wani likita ya tabbatar musu da rasuwarsa.

 An sami rahoton cewa mamacin ya kashe kansa ne bayan ya fahimci cewa tsohuwar mamatars ta sake yin aure.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories