Ƙasar Saudiyya Ta Yi Ragin Kudin Aikin Hajji Ga Maniyatan Najeriya

Hukumar Alhazan Nijeriya NAHCON) ta sanar cewa hukumomin Saudiyya sun yi ragin kudin aikin Hajjin bana 2024 ga duk masu son sauke farali.

NAHCON ta ce shugabata, Jalal Ahmad Arabi, ne ya mika bukatar a yi ragin inda ya ce ragin ya shafin kudin tikitin jirgi, masauki, jigila da sauran hidimomin da ake yi wa alhazai a kasar ta Saudiyya.

Kakakin NACHON, Fatima Sanda Usara ta sanar a ranar Laraba cewa a sakamakon haka, Saudiyya ta rage “Dala 138 daga kudin tikitin jirgin da aka biya Hajjin shekarar 2023, masauki a Madina da aka saba biyan Riyal 2,080 ya koma 1,665, masauki a Makkah ya koma Riyal 3,000 daga 3,500.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories