Ko Kun San Yawan Shan Shayi Na Hana Tsufa

Masana sun binciko cewar shan shayi na da matuƙar tasiri a jikin Ɗan Adam,Sinadarine da ke inganta lafiyar ɗan Adam .Masana sun gano cewar Yawan Shan shayi na sa tsawon rai, Haka kuma shan shayi na hana tsufa da wuri.

Ƙwararru a Hukumar Kula da gudanar da bincike akan cutar daji na kasa da kasa tare da babbar kwalejin London wato Imperial College sun gano babban muhimmanci da kuma amfanin da bakin shayi ke dashi a jikin dan adam.

Rahoton ya bayyana cewa a ta’ammali da shayi na sa tsawon rai sannan kuma yana  kariya daga kamuwa daga sauran cutuka kamar irin su Ciwon siga,Ciwon koda, da kuma Ciwon Hanta.

Haka kuma shan shayi na taimakawa wajen hana Shanyewar ɓarin jiki sannan kuma yana bayar da kariya wajen hana kamuwa da cututtuka da suka shafi zuciya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories