NDLEA Ta Cafke Wani Mai Yiwa Ƴan Ta’adda Safarar Ƙwayoyi A Maiduguri

Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa NDLEA sun cafke wani mutum mai shekaru 42 wanda ke yiwa ƴan tanada safarar ƙwayoyi a garin Maiduguri.

 Haka kuma Hukumar ta kuma kama wata mata mai ɗauke da cikin wata shida kuma uwar ƴaƴa uku,da wasu mata da laifin fataucin miyagun ƙwayoyi, a wani samamen da aka kai.

 Kamen ya faru ne yayin da hukumar ta kama sama da kilogiram 7,609 na haramtattun ƙwayoyi a jihohi takwas.

 Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi Shi ne ya bayyana Nasarar a wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi.

Babafemi ya ce, “A jihar Borno, jami’an hukumar NDLEA sun damƙe wani mutum mai shekaru 42 da ake zargi da kai wa ƴan ta’adda miyagun kwayoyi a yankin Banki da ke kan iyaka tsakanin Najeriya da Kamaru.

Ahmad Mohammed, an kama shi ne a ranar Juma’a 9 ga watan Fabrairu a shingen bincike da ke Bama.A lokacin da aka lalube kayansa, aka sami ƙwayar tramadol 20,000 a ƙoƙarin sa na safarar su zuwa kan iyaka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories