Yau Ce Ranar Rediyo Ta Duniya: Wacce Rawa Kafar Ta Taka A Rayuwarku?

Ranar 13 ga watan Fabrairu na kowace shekara ne Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin Ranar Rediyo ta duniya.

Rana ce da hukumar raya al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) ta kebe musamman don tunawa da tasirin da kafar rediyo ke yi wajen sauya rayuwar jama’a, da kuma irin rawar da take takawa wajen bayar da bayanan abubuwan da ke faruwa a fadin duniya.

Rediyo kafa ce ta ilimantarwa, fadakarwa wadda kuma ke assasa kawo sauye-sauyen manufofi a kasa ta hanyar rahotannin da ake yadawa.

Gudummuwar da Rediyo ya kawo ta fi gaban a nanata ga mutanen karkara da na birni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories