Wani Zaki Ya Yagalgala Mai Kula Da Shi Har Lahira A jami’ar Awolowo

Wani zaki da ake kiwo a wurin ajiye dabbobi da ke Jami’ar Awolowo ya Kashe mai kiwon sa mai suna Mista Olabode Olawuyi har lahira yayin da yake ba shi abinci.

 Olabode ya kasance masanin fasahar dabbobi a jami’ar Obafemi Awolowo, Wanda ya shafe shekaru goma yana kula da  dabbobi.

 Jami’in hulda da jama’a na jami’ar, Abiodun Olarewaju, Shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin.

 Ya ce, “Mista Olawuyi ya kasance yana kula da zakin tun lokacin da aka haife su a makarantar kimanin shekaru 9 kenan abin mamaki sabo bai hana wannan zaki ya farwa mai kula da shi ba.

 Ko da abin ya faru Sauran ma’aikatan da ke wurin yayin faruwar lamarin sun yi iya bakin ƙoƙarin su dan ganin sun ceto shi amma abin yaci tura wanda hakan yayi sanadin rayuwar sa .

 ”Cikin ɓaci rai an yiwa wannan zaki kisan gilla.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories