Kotu Ta Bayar Da Umarnin Yiwa Murja Kunya Gwajin Ƙwaƙwalwa

Wata kotun shari’ar Musulunci a Kano ƙarƙashin mai Shari’ah Mallam Nura Yusuf Ahmad tayi umarnin a kai Murja Kunya wajan Likitan ƙwaƙwalwa domin duba lafiyar ƙwaƙwalwar ta la’akari da yanayin maye da kotun tace ta lura tana ciki.

A makon da ya gabata ne kotun ta bayar da umarnin a tsare Murja a gidan gyaran hali na Kurmawa bayan da Hukumar Hisbah ta kama ta bisa zargin nuna rashin ɗa’a da yunƙurin jefa ƴan mata cikin karuwanci.

Kotun dai ta nemi a tsare ƴar Tiktok ɗin ne har zuwa ranar Laraba 27 ga watan Fabarairu sai dai bayanai na cewa an bayar da belin ta, lamarin da ya fusata wasu al’ummar jihar.

Hukumar Hizba a jihar Kano dai na tuhumar Murja Kunya da razana al’umma, ayyukan baɗala, tayar da hatsaniya, tayar da hankalin al’umma, kawo ɓatagari cikin unguwa, iƙirarin cewa ita ce shugaban karuwai da ƴan kwalta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories