NDLEA Ta Yaba Da Goyon Bayan Tinubu Kan Yaƙi Da Shan Miyagun Ƙwayoyi

Shugaban kuma babban jami’in hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa Brig. Janar Mohamed Buba Marwa (Mai Ritaya) ya bayyana jin daɗinsa ga irin yadda jami’an hukumar yaƙi da muggan ƙwayoyi su ka sami goyon bayan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa ƙoƙarin da ake yi na daƙile matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da kuma safarar su a faɗin ƙasar nan.

 Shugaba Marwa ya bayyana haka ne a lokacin da ansa tambayoyi daga ƴan jarida a lokacin da yake duba kayayyakin aiki a barikin NDLEA da ke Yola, wanda ya ce a yanzu haka aiki zai fara gudana a wurin. 

 A cewarsa, “Mun gode wa Allah da ya ba mu ikon kammala wannan aiki sannan kuma mun yaba da yadda ake ci gaba da gudanar da ayyuka. Shugaban ƙasa ya yaba da al’amuran da suka shafi tsaro da jin daɗin ma’aikata. Jami’ai na ƙoƙarin wajen kame, gurfanar da masu laifi, amma duk da haka masu laifi suna farmakan ma’aikata saboda rayuwa da suke a cikin su.  Amma yanzu jami’an mu sun sami bariki.Tun zamanin shugaba Buhari aka amince da gina shi kuma a yanzu haka Shugaba Tinubu ya ɗauka daga inda ake tsaya saboda haka muna matuƙar godia da jin daɗi irin yadda aka samu da hukumar NDLEA.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories