Hanyoyin Da Mace Za Ta Bi Wajen Janyo Hankalin Mijinta Cikin Sauki

Yana daga cikin dabi’u na mata, neman hanyar da za su mallaki miji. Amma sai dai Irin wannan lamari kan ba wasu mata matsala wajen rashin gane yadda za su bi su mallaki miji cikin sauki. Uwargida ga hanyoyi mafi sauki da zaki bi wajen samun hankalin miji wanda aka tsara su bisa koyarwa Addini, Kamar yadda malaman addini ke nasiha da tuni kan cewa, Aljannar mace na karkashin kafar mijinta.

Daga cikin waɗannan halayyar ana so mace ta kasance:

-Ya kasance duk maganar da zai fita daga bakinki uwargida mai dadi ne a kunnen mijinki wanda zai sa shi murmushi da jin dadi.

-Uwargida Ki kasance mai sakin fuska ga mijinki a duk lokacin da ya shigo gida ya same ki cikin frinciki 

-Sannan kuma Ki kasance a kullum kina ɗaukar mijinki tamkar sarki ne ta wurin mutunta shi, da juriya wajen daukar laifinsa ya dawo kanki saboda bashi girma ko da ke ce da gaskiya.

-Uwargida Kar ki kasance kullum a cikin bacin rai ko fushi da mijinki, domin fushi shi ne kofar kowacce sharri.

-Kar ki kasance mai girman kai wajen bashi haƙkokin zamanku, abin da yake so ko da baki so matuƙar bai sabawa addini ba ki yi mishi.

-Sannan kuma Ki nuna wa mijinki komai naki nashi ne komai nashi kuma naki ne, ki nuna baki da iko a kai sai abin da ya yi.

-Ki kasance mai kula da abubuwan da yake dubawa a jikinki in ya shigo gida, ina idonsa ya ke yawan kallo a jikinki bayan kin yi kwalliya. Idan kirji ne sai a gyara mashi su da kyau. Idan bayanki yake kallo sai nan ma a gyara domin a dauke masa hankali. In kuma kin tabbatar duk lokacin da ya dawo yana neman buta ne, to ki kula da sanya ruwa a cikin butar.

KARANTA KUMA: Mafi Yawan Tambayar Da Mata Ke Yi Wa Miji A Zamantakewar Aure Shi ne “Me Za A Dafa”

-Ki kasance mai yawan godiya kan duk abin da ya kawo miki gida komin kankantar abin kar ki raina, sannan ki nuna masa kokarinsa a kan duk abinda ya kawo.

-Kar ki sake ki yi ƙasa a guiwa wajen girmama duk wadanda kika san yana girmama su, kama daga iyaye har zuwa ƴan uwa da abokan arzikinsa.

-Uwargida Kar ki yawaita tambayarsa daga ina kake ko me kake yi sai yanzu kake dawowa? waɗannan tambayoyi na lalata zamantakewa.

-Haka kuma Ki kasance mai ɓoye sirrinsa wajen iyayenki da sauran al’umma.

-Sannan kuma kar ki yadda duk lokacin da ya kiraki ki kawo masa wani abu ki tura wani ko wata ta kai, ki je ki yi da kanki.ki kasance hidimar sa itace kan gaba a duk abinda za kiyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories