Yadda Mace Za Ta Kiyaye Cutar Sanyi A Jikinta

Cutar sanyi cuta ce da kusan kowace mace ba dauke dashi,ita wannan cuta ta sanyi tana da matukar illa ga lafiyar ƴa mace har ma da Da namiji.

Ya kamata ace uwargida ta san cewa akwai hanyoyi daban-daban da ka iya kawo wanan cuta ,wanan cuta an san cewa idan tayi tasiri a jikin mutun to tabbas yana haifar da illoli kamar rashin haihuwa,wanda wannan tabbas babbar illa ce
Akwai abubuwa daban daban da ya kamace uwargida ta kiyaye don ganin ta kaucewa kamuwa da wannan cuta, wadannan hanyoyi sune kamar haka:

-Uwargida ta kiyaye yawo a tsakar gida babu takalmi da yawa mata sunada wannan dabi’a ta yawo babu takalmi wanda kuma hakan illace sosai.Ba cutar sanyi kadai ba akwai wasu boyayyun cuttuka da ba a san da su ba duk suna iya samun mafaka a jikin mace.

-Yawo babu Dan kamfai rashin saka pants yakasance wata babbar dabi’a da mata suka daukarwa kansu wanda hakan kuma illa ce ga lafiyar Dan Adam,mace ana so ta kasance mai killace jiki domin hakan na magance cuttuka da dama.

-Saka jikakken zani ko dan siket shima wanan ana so mace ta kiyaye sa ,saboda yanda kike zaune da wannna jikaken zanin to fa haka sanyi zai dinga bin jikin ki yana bin jijiyo har yaci karfn jiki yayi illa.

-Zama a kasa ba bu shimfiɗi hakan illace sosai ga lafiyar mace,ya kamata uwargida ta sani cewa ba ko ina bane zata je ta zauna ya kamata ta san a kan meya kamata ta zauna,ana bukatar kujera ko dai wani abu mai laushi amma kar uwargida ta dinga zama a budadden wurin kamar saman siminti ko kuma tiles,saboda jikin mace halittace da ake son ta cikin dumi ko yaushe.

Idan uwargida za ta kiyaye waɗannan sharuɗɗa sannan kuma ta kasance tana yawan ziyartar likita domin neman shawrwari da sauran abubuwa to fa zata rage illar cutar sanyi a jikinta sosai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories