Ina Baƙin Cikin Halin Da Ƴan Najeriya Ke Ciki:Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya ce yana sane da tsananin matsi da wahala da ƴan Najeriya ke ciki sakamakon wasu manufofin da gwamnatinsa ta ɗauka.

 Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci Reuben Fasoranti, jigo a kungiyar siyasa da zamantakewa ta Pan-yoruba, Afenifere, a gidansa da ke Akure, babban birnin jihar Ondo.

Daily Trust ta ruwaito cewa, shugaba Tinubu ya kai wannan ziyara ne a tafiyar Ta’aziyya da ya je wa iyalan Gwamna Rotimi Akeredolu.

 Dare Ajayi, kakakin kungiyar Afenifere, wanda ya halarci taron, ya bayyana cewa shugaba Tinubu Na iya ƙoƙarin sa wajen ganin ya kawo ƙarshen matsi da ake ciki.

 “Irin wahalar da ƴan Najeriya ke fuskanta, shugaba Tinubu yasan irin matsin da ‘yan Najeriya ke ciki kuma ya ce nan ba da jimawa ba Najeriya za ta shawo kan lamarin.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories