NPFL ta ci tarar Niger Tornadoes Naira Miliyan 3 saboda karya dokokin gasar Firimiyan Najeriya

Hukumar shirya gasar firimiyar najeriya NPFL Ta Ci Tarar Niger Tornadoes Naira Miliyan 3 saboda karya dokokin gasar a wasansu na ranar 23 da suka yi da Rangers.

An tuhumi Niger Tornadoes da laifin karya tsari da ka’idojin NPFL a wasansu na mako na 23 da suka buga da Rangers.

Haka kuma jami’an kungiyar Tornadoes da wasu mutane ba tare da izini ba, suka yi kutse cikin filin wasan yayin karawar ta su Rangers ranar Lahadi (3 ga Maris, 2024).

An kuma Kara tuhumar kungiyar Niger Tornadoes da laifin rashin gudanar da ayyukansu Yadda ya kamata wanda ka iya kawo tsaiko ga wasan.

Saboda haka aka ci tarar kungiyar Naira miliyan 1 na gaza samar da ingantaccen tsaro.

Sannan Tornadoes za ta sake biyan tarar Naira miliyan 1 saboda kutsawa cikin filin wasa ba tare da izini ba.

Bayan haka za su kara biyan tarar Naira miliyan 1 saboda nuna halin rashin da’a.

Niger Tornadoes na da sa’o’i 48 daga lokacin da aka fitar da wannan sanarwar domin daukaka kara ko karbar wadannan takunkumi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories