Dan wasan Super Eagles na Najeriya Victor Boniface zai dawo taka leda kafin karshen shekara.

Labarin da ke fitowa daga BayArena na Bayer Leverkusen da ke buga gasar Bundesliga a Jamus, ya nuna cewa dan wasan Super Eagles na Najeriya Victor Boniface da zai dawo taka leda kafin karshen shekara.

Boniface ya samu rauni ne a lokacin da yake sansanin Super Eagles da ke shirin tunkarar gasar cin kofin Afrika ta 2023.

Bayan an yi masa tiyata cikin nasara, dan wasan ya fara atisaye domin murmurewa.

Sabon bayani daga likitocin kulob din sun nuna cewa Boniface zai dawo ranar 30 ga Maris a karawarsu da Hoffenheim ko kuma 3  ga watan Afrilu a  wasansu da Fortuna Dusseldorf.

Boniface ya ci kwallaye 10 a wasanni 16 kafin ya samu rauni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories