Tinubu Ya Dakatar Da Babban Daraktan Hukumar Raya Wutar Lantarki

Shugaba Bola Tinubu ya rattaɓa hannu kan dakatar da Babban Daraktan Hukumar Raya Wutar Lantarki (REA) Ahmad Salihijo Ahmad tare da wasu manyan Daraktocin hukumar su Uku,Waɗanda suka haɗa da  Olaniyi Alaba Netufo,Barka Sajou , Sa’adatu Balgore

 Dama kuma an sami rahoton cewa Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da ƙwaƙƙwaran bincike kan ayyukan ma’aikatan da aka dakatar inda ake zargi su da karkatar da maƙudan kuɗaɗe sama da Naira biliyan 1.2 a cikin shekaru biyu da suka wuce. 

Tuni dai Hukumar EFCC ta Yi nasarar ƙwato wasu daga cikin kuɗaɗen da aka karkatar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories