A Shirye Na Ke In Gana Da Ƴan Bindigan Da Suka Sace Ɗaliban Kuriga-Gumi

Fitaccen Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce a shirye ya ke tsaf ya yi zama da ƴan ta’addan da suka yi garkuwa da yara ƴan makaranta a garin Kuriga su 287 da kuma na Firamare LEA da ke ƙaramar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna.

 A cikin wata sanarwa da tawagar sa suka bayyanawa manema labarai sun ce Sheik Gumi ya bayyana aniyarsa na taimaka wa gwamnati wajen tattaunawa da ƴan bindigan don a sami damar kuɓutar da ɗaliban da aka sace.

 Haka kuma Malammin ya nuna takaicin sa game da matakin da gwamnati ta ɗauka na ƙin zaman tattaunawa da ƴan bindiga.

Malamin ya ce tattaunawa da ƴan bindiga ita ce hanya mafi a’ala na samun damar sako waɗanda aka sace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories