Mohamed Elneny ya kaddamar da dakin yin Sallah ga ‘yan wasan Arsenal a cikin filin wasa na Emirates.

Dan wasan tsakiyar Arsenal, Dan kasar Masar Mohamed Elneny ya kaddamar da dakin yin Sallah ga ‘yan wasan Arsenal a cikin filin wasa na Emirates.

Dakin addu’o’in na addinai zai bawa ‘yan wasan kirista da musulmi na kowace kungiya damar yin addua a lokacin wasannin da za a yi a filin wasa na Arewacin London.

Kaddamar da shirin ya zo ne yayin da al’ummar musulmi a fadin duniya ke fara azumin watan Ramadan a ranar Litinin.

Elneny musulmi ne mai kishin addini wanda kullum yake yada akidarsa ta addinin musulunci a kafafen sada zumunta ta hanyar karanta qur ani a bidiyo.

Yana daya daga cikin ‘yan wasan da suka fi dadewa a kungiyar ta Arsenal tun bayan da ya koma kungiyar a shekarar 2018 inda kwantiraginsa zai kare a karshen watan Yunin 2024.

Dan wasan mai shekaru 31, ya buga wa Gunners wasanni uku kacal a gasar Premier a bana, kuma gasarsa ta karshe tun daga watan Agustan 2022 da Fulham.

Tauraron dan Masar din zai iya buga wasansa na uku a gasar cin kofin zakarun Turai a ranar Talata lokacin da Mikel Arteta za su karbi bakuncin Porto a wasan da za a yi a zagaye na 16.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories