Tennis: Novak Djokovic ya sha kashi a hannun Luca Nardi mai shekaru 20 a gasar Indian Wells

Dan wasan Tennis na Duniya Novak Djokovic ya sha kashi a hannun Luca Nardi mai shekaru 20 a zagaye na uku na gasar Indian Wells.

Nardi dan kasar Italiya mai lamba na 123 a duniya, tun da farko an yi waje da shi a wasan neman gurbin shiga gasar amma a karshe ya samu kaiwa ga gasar bayan da wani dan wasa ya janye daga gasar.

Ya samu nasarar doke zakaran Grand Slam karo 24 da ci 6-4 3-6 6-3,nasarar da ta daga darajarsa a yanzu.

Nardi zai kara da Tommy Paul ne a zagaye na 16, bayan da Ba’amurken ya samu nasarar doke Ugo Humbert na Faransa da ci 6-4 6-4.

Daniil Medvedev ya doke Sebastian Korda da ci 6-4 5-7 6-3 inda zai kara da Grigor Dimitrov a zagaye na gaba.

Holger Rune, Casper Ruud da Taylor Fritz suma sun tsallake zuwa zagaye na 16 a gasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories