Ana Tsaka Da Azumi Wani Ya Ɗirkawa Ƴar Shekara 9 Fyaɗe Kuma Ya Kashe Ta 

Daga Halima Lukman

A Jihar Filato ne, aka wayi gari da mummunan lamari inda wani mutum ya yi wa wata yarinya ƴar shekara tara fyaɗe sannan kuma ya kashe ta, ta hanyar rataya.

Yarinyar da tsautsayin ya rutsa da ita mai suna Nana Abubakar Yakubu, rahotanni sun bayyana cewa yarinyar ƴar unguwar Isyaku gwamna ne da ke garin Jos.

A zantawa da aka yi da mahaifiyar yarinyar tace “Na zo na samu ƴata a kwance a wani lungu, da taimakon wani makwabcinmu muka ciciɓeta zuwa asibitin Malam Haris,”.

Mahaifiyar takara da cewa ko da muka Kaita asibitin a nan ne aka tabbatar da mutuwar ta.

 “Likita ne ya tabbatar mana da cewa an mata fyaɗe tare da nuna mana shafin igiyar da ke wuyan ta.” Mahaifiyar ta ƙara da ccea wanda ya mata fyaden ya kashe ta ne saboda ya fahimci ta gane shi a

A nasa jawabin Mahaifin Nana mai suna Abubakar Yakubu, ya shaida wa gidan radion unity FM dake garin Jos cewa, “Na aiketa ta siyo mangyada sai ta jima ba ta dawo ba, sai na aika ‘yaruwar ta, ta duba inda suke wasa sai ta dawo da ihu da kuka wai an kashe ta”.

WikkiTimes ta tattaro cewa, Mal Abubakar ya ce wanda su ke zargi shi ne kaninshi domin ana raɗe-raɗin ɗan shan jini ne .

Yayin haɗa rahoton an nemi jin ta bakin Kakakin Ƴan sandan jihar ta Filato amma abin ya ci tura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories