Hajjin Bana: Maniyyatan Najeriya Na Fuskantar Barazanar Rashin Samun Damar Sauke Farali

Majalisar Koli Tabbatar da Sharia”r Musulunci ta Najeriya ta bayyana damuwa a game da barazanar da aikin Hajjin bana ke fuskanta, biyo bayan labarin da ke cewa akwai yiwuwar maniyyatar kasar ba za su samu damar sauke farali a bana ba.

Binciken da majalisar ta gudanar kan shirye-shiryen aikin Hajjin na bana ya nuna akwai wagegen giɓi a game da shirye-shiryen.

Wata sanarwa da majalisar ta fitar, wadda ta samu sa hannu sakatarenta, Nafiu Baba Ahmed ta ce wa’adin da hukumomin Saudiyya suka ɗiba game da kammala shirye-shiryen da suka kamata, kama daga biyan kuɗin kujera zuwa sauran shirye shirye, na iya cika ba tare da maniyyatan sun san halin da suke ciki ba na ainihin kuɗin da ya kamata su cika kan kujerar.

Majalisar ta ce har ya zuwa wannan lokacin ba a biya kuɗin rabin kujerun da aka ba wa Najeriya ba.

Daga bisani majalisar ta ce tana sane da irin ƙoƙarin da gwamnati ke yi wajen samun sauki musamman kan batun canjin dala wanda shi ne musabbabin wannan matsalar.

Ta kuma buƙaci ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da kuma masu ruwa da tsaki da su taimaka yadda ya kamata domin ganin ba a samu koma baya a aikin Hajjin bana ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories