Babu Jirgin Koyon Tuƙi Ko Ƙwaya Ɗaya A Kwalejin ‘Aviation’ Da Ke Zaria-Cewar Imalighwe

Mukaddashin Shugaban Kwalejin Fasahar Jiragen Sama ta Najeriya, NCAT, da ke Zariya, Shaka Imalighwe, ya fito ya bayyana cewar fa kwalejin batada jirgin horar da ɗalibai ko ƙwaya ɗaya.

 Mista Imalighwe ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis yayin da ake gudanar da zaman bincike kan sayar da jirage masu saukar ungulu guda biyu da aka yi a Abuja.

 Mista Imalighwe ya shaidawa kwamitin majalisar wakilai Cewar fa shi an bashi ragamar tafiyar da kwalejin ne a matsayin muƙaddashi a watan Janairun 2024.

Ya, ƙara da cewa duk da dai shi ne mataimakin shugaban kwalejin a lokacin da aka yi Gwanjon jiragen amma sam bashida hannu a cikin lamarin .

 Da yake mayar da martani, shugaban kwamitin, Ademorin Kuye, ya nuna matuƙar damuwarsa kan yadda aka wawure jiragen aka sayar wa wasu tsirarun mutane aka bar kwalejin holoƙo babu komai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories