WIKKIDATA: Yadda Ƙananan Hukumomi Su Ka Karɓi Sama Da ₦Biliyan 270

Wani bincike da WikkiTimes ta yi ya nuna cewa jihohin Arewacin Najeriya sun samu Naira biliyan 278 a matsayin kason ƙananan hukumomi a watanni biyun farko na shekarar 2024.

Binciken ya nuna cewa jihar Kano ta samu Naira biliyan 29.8 sai jihar Katsina wadda ta samu Naira biliyan 22.1.Mafi ƙarancin kudin da ake samu na jihohin Arewa maso gabashin Najeriya, inda jihar Gombe ce ta samu adadin Naira biliyan 8 a watanni biyun farko na shekarar 2024.

A yankin Arewa maso yammacin kasar nan kuwa, jihar Kaduna ta samu mafi yawan kudi inda ta samu Naira biliyan 16.5 sai kuma jihar Kano wadda ta samu Naira biliyan 15.9.Jihar da ta samu mafi ƙarancin kudi a yankin Arewa maso Yamma ita ce jihar Jigawa inda ta samu Naira biliyan 8 a matsayin kason ƙananan hukumomi na watanni biyu na farkon shekarar 2024.

A yankin Arewa ta tsakiya kuwa, jihar Niger ce ta samu mafi yawa inda kudin ya kai Naira biliyan 16.5 sai jihar Benue da ta samu Naira biliyan 15.9.A shiyyar Arewa maso Gabas kuwa jihar Borno ta samu Naira biliyan 17.7, sai jihar Bauchi ta samu Naira biliyan 15.2, sai kuma jihar Adamawa da ta samu Naira biliyan 13.4.

Kasafin kudin jihar Kano za a kashe Naira miliyan 50 a shekarar 2024 don gina makarantu. Hakan na nufin adadin Naira biliyan 29.8 da aka samu a matsayin kason kananan hukumomi na watanni biyu na farkon 2024 zai iya gina makarantu guda 596 a faɗin jihar.

KU DUBA: Rahoto Na Musamman: Duk Da Irin Maƙudan Kuɗaɗen Da Ake Warewa Tsaro A Zamfara Amma Har Yanzu Matsalar Na Cigaba Da Ta’zzara

Kasafin na watanni biyun farko na shekarar 2024 ya zarce adadin da aka warewa ma’aikatar albarkatun ruwa na shekarar kasafin shekarar 2024 a jihar.

Cikakkun bayanai sun nuna cewa jihar na shirin kashe Naira biliyan 5 domin samar da albarkatun ruwa a shekarar 2024, yayin da a watanni biyun farko na shekarar 2024, ta samu Naira biliyan 7.7 a matsayin kasafi.

Adadin kudaden da jihar Kaduna ta samu kuwa a cikin watanni biyu (N18.2bn) ya zarce Naira biliyan 3 da aka ware wa ma’aikatar harkokin ƙananan hukumomi a shekarar 2024.

Gudanar da rabon ƙananan hukumomi ya kasance batun da ke jawo cece-kuce a Najeriya. Kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta kasa (NULGE) ta zargi jihohi da rashin sarrafa kudaden kananan hukumomi yadda zai amfani al’ummar yankunan karkara.

KUNA IYA DUBA: Ƴan Majalisun Arewacin Najeriya Sun Zargi Godswill Akpabio Da Aikata Ha’inci

Haka kuma idan dai ba a manta ba ko a shekarar 2020 sai da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan wata dokar cin gashin kan kananan hukumomi a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories