Ƴan Sanda Sun Kama Mutum 4 Bisa Yinkurin Ƙona Sansanin Ƴan Gudun Hijira

Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta gurfanar da wasu mutane huɗu da ake zargi da yunƙurin cinna wuta a sansanin yan gudun hijira da ke Mafa a jihar Borno.

 Sunayen waɗanda ake zargin su ne Malum Usman mai shekaru 16;  Bulama Bukar, 14;  da Rawa Usman, 11;  wanda ake zargin wani Babagana Umar mai shekaru 40 shi ne ya ɗauki nauyinsu.

 An sami rahoton ne a lokacin da wata kungiyar mafarauta a Mafa ta kai rahoto ga ƴan sanda cewa an kama waɗanda ake zargin da ashana a lokacin da suke kokarin bankawa wani gida wuta a sansanin ƴan gudun hijira a ranar 24 ga watan Maris, 2024, da misalin karfe 10:30 na safe.

ASP Kenneth Nahum Daso, ya ce sun gano cewar Babagana Umar ya ce zai biya waɗannan yara kuɗi Naira 10,000.Sai dai wanda ake zargin ya musanta.Inda yanzu haka ƴan Sanda na gudanar da bincike. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories