Sheik Musa Lukwa Limamin Da Ya Gudanar Da Sallar Idi A Yau

A yau Talata ne  wani malamin addini Sheikh Musa Lukwa, mazaunin garin Sokoto ya jagoranci mabiyan sa wajen gudanar da sallar idi.

 Duk da cewar a jiya Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci na Najeriya (NSCIA) ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ta ce ba a ga watan sallah ba a jiya Litinin inda ta ayyana ranar Laraba a matsayin farkon watan Shawwal kuma ranar Idi.

Amma duk da haka Malam Lukwa wanda dama tsawon shekaru, yana bijirewa umarnin Sarkin Musulmi kan ganin wata, In da ya yi kunnen uwar Shegu ya jagoranci sallar Idi a masallacin Juma’an sa da misalin karfe 8:30 na safe.

 Da yake ƙara jawabi Malam Lukwa ya ce tun da dai an ga wata a makwabtan Najeriya wato Nijar shiyasa yayi Sallah.”Kuma indai za a ga wata a Saudiyya mu yi Sallah to me zai sa ba za mu bi Nijar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories