Riftawar Tsauni Ya Yi Ajalin Wasu Almajirai A Jihar Kebbi

A jiya Asabar 21 ga Afrilu 2024 aka sami rahoton Riftawar wani Tsauni a kan wasu almajirai su takwas a jihar Kebbi da misalin Ƙarfe 12 na rana.

Rahotanni sun bayyana cewar Almajiran sun fito ne daga Tsangayar Malam Dan-Umma da ke Bayan Science, Badariya  a Jihar Kebbi.

Ko da Wikkitimes ta sami zantawa da wani mazaunin yankin mai suna Abubakar Muhammad ya bayyana cewa ”shi wannan dutsen muna kiran shi da Dutsin Dukku ,yana ta wajen gari ne mutane suna zuwa dibar ƙasar dake jikin dutsen don amfani dashi wajen Gini to Suma almajiran wannan kasar ta Dutsin itace sukaje nema a wajen inda suna cikin Saran wannan Dutsen ne sai ya Rufto akansu”

Faruwar iftila’i ya yi sanadiyyar mutuwar Almajirai 7 inda ɗaya da ya rayu shikuma ke kwance a asibiti yana karɓar kulawa.Tuni dai .aka yi jana’izar sauran kamar yadda Addini ya tanadar

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories