NAFDAC Ta Ƙwamushe Jabun Kayyaki Na Kimanin Miliyoyi A Wani Samame Da Ta Kai A Abuja

Hukumar NAFDAC a wani samame da ta kai kantunan Sahad da H-Medics da sauran kasuwannin da ke Abuja, ta yi nasarar kama jabun kayayyakin kwalliya na kimanin Naira miliyan 50.

Hukumar ta kai samamen ne a manyan kantunan Wuse 2 da Gwarinpa a birnin tarayya Abuja, inda suka gano jabun kayayyaki.

  Haka kuma hukumar ta ziyarci kasuwannin Garki, Wuse, Utako, Kugbo, Nyanya da Mararaba, inda nan ma suka yi nasarar ƙwace jabun kayan kwalliya da magunguna.

A ƙarshe Hukumar ta sake jaddada aniyar ta na kawar da masu Safarar Jabun kayayyaki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories