Kotu Ta Ɗaura Tarar Naira Miliyan 300 Ga ‘Yan Sandan Da Suka Farwa Ƴan Shi’a

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kaduna ta umurci hukumar ƴan sanda da su biya zunzurutun kuɗi har Naira miliyan 300 ga iyayen ƴan Shi’a uku da ake zargin jami’anta sun kashe a lokacin da suke gudanar da muzaharar shekarar 2022 a Zariya.

 Mai shari’a Hawa Buhari, a cikin hukuncin da ta yanke, ta ce “haƙƙoƙin na su an tanada shi a cikin sashe na 33, 38, 39, 40, 42 da 46 na kundin tsarin mulkin 1999   Umarni na 2, Dokokin 1, 2, 3, 4, 11 da 12 na Dokokin Haƙƙin Mahimmanci (Tasirin Tilasta) Dokokin 2009;  Ana aiwatar da doka ta 4, 8, 10, 11 da 12 na Yarjejeniya Ta Afirka ta 2004 game da ƴancin ɗan adam da jama’a.”

Mai shari’ar ta jaddada cewar adadin Naira miliyan 100 ya zama tilas a biya duka iyayen uku, inda za a biya jimillar Naira miliyan 300 kenan, a matsayin diyya, kuma za a rika samun ribar kashi 10 cikin 100 a duk shekara har sai an gama biyan kudaden.

 Mai shari’a Buhari, a hukuncin da ta yanke a ranar 22 ga Afrilu, 2024, wanda aka fitarwa da manema labarai kwarin a ranar Lahadi a Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories