Masu Zanga-Zanga Sun Yi Wa Sakatariyar APC Tsinke,Sun Nemi Ganduje Ya yi Murabus

Ƴaƴan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da Suka fito daga yankin Arewa ta tsakiya ƙarƙashin jagorancin Mohammed Mahmud Saba, a yau Alhamis sun hallara a sakatariyar jam’iyyar .

Rahotanni sun bayyana cewa masu zanga-zanga sun hallara ne don nuna rashin goyon bayan su ga Shugabancin Abdullahi Umar Ganduje inda suka buƙaci da ya sauka daga kujerar Shugabancin jam’iyyar .

 Lamarin ya biyo bayan matakin da babbar kotun jihar Kano ta ɗauka na dakatar da Ganduje, inda har yanzu ake ci gaba da matsa masa lamba kan sai ya ajiye muƙamin sa na shugaban jam’iyyar.

Masu zanga-zanga dai an gamsu ne ɗauke da al’umma a rubuce an sa ”Dole Ganduje ya sauka,Kuma muna so mulkin jam’iyya ya dawo yankin Arewa ta tsakiya.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories