Dalla-dalla: NLC ta fayyace dalilin kayyade N615,000 a matsayin mafi karancin albashi

Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) tayi bayani dalla-dalla akan dalilinta na neman gwamnati ta biya ma’aikata Naira dubu dari shida da dubu goma sha biyar (N615,000) a matsayin mafi karancin albashi.

A ranar Talata, 1 ga watan Mayu, gwamnatin tarayya ta bayyana amincewa da kara kaso 25 da kaso 35 a matsayin Karin albashi ga ma’aikata wanda ya fara aiki daga watan Janairu na shekarar 2024. Sanarwar tazo ne a ranar bikin ma’aikata ta wannan shekara.

Sai dai, kungiyar NLC tayi watsi da Karin albashin da gwamnatin tarayya tayi tare da bayyana cewa gwamnatin tayi gaban kanta, ba tare da yin tuntuba ba, kafin sanar da Karin.

NLC ta bayyana cewa tana son gwamnati a matakin tarayya da jihohi ta mayar da mafi karancin albashi ya koma N615,000 matukar so ake ma’aikaci ya samu rangwame na wannan tsadar rayuwa da ake fama da ita.

A ranar Alhamis ne NLC ta bakin shugabanta na kasa, Joe Ajaero, tayi Karin haske tare da bada lissafin da suka yi kafin neman gwamnati ta biya N615,000 a matsayun mafi karancin albashi. NLC ta ce muhalli zai ci N40,000 a kowanne wata.

Wutar lantarki zata lashe N20,000, kudin ruwa N10,000, Kalanzir ko Gas zai ci N35,000, kudin abinci N270,000 ( a matakin kullum N9,000), kudin kula da lafiya N50,000, sutura N20,000.

Kudin makaranta N50,000, tsaftar muhalli N10,000, sai kuma zirga-zirga da zata ci N110,000 wanda sune idan aka hada jimilla zasu tashi N615,000 kamar yadda NLC ta bayyana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories