Yadda Bincike Ya Gano Muhimmancin Zobo Ga Masu Cutar Hawan Jini

Al’ummar ƙasar Hausa sun yi amanna da Zobo, wanda a turance ake ce masa Hibiscus, Shi Dai zoɓo an Yi Ittifaqi cewr sinadari ne da ke magance hauhawar jini.

 Me bincike ya nuna ?Tabbas bincike ya nuna cewa Zobo na da tasiri wajen magance cutar hawan jini.

 Zamani mai Tsayi Zobo, sanannen abin sha ne a musamman a Arewacin ƙasa Najeriya wanda ake samo shi daga busasshen furannin jikin Hibiscus. Mai kuɗi da talaka kowa na iya mallakar zoɓo ki ɗan amfanin gida ko kuwa don sha’ani.  Zoɓo Ana noma shi ne a Arewacin Najeriya.

 A Wani bincike da aka gudanar a kwanakin baya,an yi iƙirarin cewa Zobo na da matuƙar tasiri wajen ragewa tare da sarrafa hauhawar jini a ga masu jinya da ke fama da Hawan Jini. 

A shekarar 2023, kungiyar Hibiscus Flower Exporters na Najeriya ta yi hasashen kimanin ana samun kuɗin shiga na kimanin ton N48bn na kusan Naira miliyan 1.7.  A duk shekara, Najeriya tana fitar da kimanin kwantena 1,983 na zoɓo wanda tsayinsa ya kai kusan ft 40, kwatankwacin kusan metric ton 23,796.

A wani faifan bidiyo da ya bayyana wani Abubakar Isah, mazaunin garin Gombe, ya bayyana  cewa, tabbas zoɓo na maganin bawan jini ku  Tun daga wannan lokacin, wannan bidiyon ya haifar da ra’ayoyi kusan 678 da dangwali 26.

 Idan aka yi la’akari da yadda ake da zoɓo a ƙasa Najeriya manyan masu bincike sun yi kokarin tabbatar da ingancin amfanin sa domin gujewa maimaita abinda ya faru lokacin cutar Ebola da aka dinga wanka da gishiri.

 Don tabbatar da da wannan bincike ya sa jaridar, WikkiTimes ta faɗaɗa binciken ta game da tasirin Zobo wajen maganin hawan jini.

 Wani binciken da aka buga a cikin Journal of Advanced Pharmaceutical Technology and Research ya nuna cewa yin shayin zoɓo tabbas yana rage yawan jini musamman waɗanda hawan jinin su ke matakin farko. Sakamakon binciken ya ba da shawarar shan shayin hibiscus mai tsami sau biyu a rana don masu ciwon hawan jini na mataki na ɗaya.

 Hakazalika, wani binciken ya sake nuna cewa zoɓo yana rage yawan jini kuma yana daidaita yawan jini musamman masu mataki na farko na hawan jini da kuma masu systolic.  Saboda haka bincike ya nuna cewa zoɓo bashi da wata illa  gamasu cutar bawan jini.

Dr Sani Giade na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa Bauchi (ATBUTH) ya ce Zoɓo lafiyayyen abin sha ne yana fi lafiya fiye da sauran abin sha da ake saidawa na kwali.

 “Hibiscus yana da fa’idodin kiwon lafiya, ga masu hawan jini.  Hakan na nufin yana rage hawan jini,” inji shi.

Haka shima Dokta Hassan Shu’aibu na ofishin inshorar lafiya ta ƙasa da ke Bauchi ya ce Zoɓo na da matuƙar amfani ga lafiyar ɗan Adam.

 nuna cewa yana ƙara ruwa a jiki .Rashin ruwa a jiki yana ɗaya daga cikin hanyoyin da ke haifar da hauhawar jini.Sabods Haka zoɓo yana iya amfani dashi wajen magance Hawan jini.

A ƙarshe dai bincike da bayanan kimiyya ya tabbatar da cewa ana iya amfani da zoɓo wajen magance Hawan jini.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories