Gwamnatin Bauchi Ta Wanke Kanta Game Da Riftawar Gini Akan Wasu Ɗalibai

Azuzuwan ginin laka da ake raɗe-raɗin ya Rufta da ɗalibai ba gaskiya bane wanda ake ƙaryar cewa lamarin ya faru ne a ƙaramar hukumar Toro ta jihar Bauchi,hasalima mutanen da suka bayyana a cikin bidiyon da aka gani ko kusa basu da alaƙa da mutanen Bauchi.

 A binciken da Wikktimes ta yi ta gano gaskiyar zance.

 Dokta Jamila Mohammed Dahiru, kwamishinan ilimi na jihar Bauchi, a ranar 16 ga Maris, 2024, a wani faifan bidiyo ta fito  ta musanta wannan lamari.

 “Bidiyon makarantar da ke yawo ko kusa ba ɗaya daga cikin makarantu mu ba ne,” in ji ta.  Kwamishinan ta musanta faifan bidibidiyo ta na mai cewa, “Yaren da mutanen cikin wannan bidiyo ke yi ba Yaren mutanen Bauchi ba ne.”

Mujallar Tozali, ita ta saka wannan faifan bidiyo a shafinta na Facebook a ranar 15 ga Maris 2024 inda aka ga katangar wani aji na ruguzowa akan ɗalibai wanda aka gina ta da laka Wannan bidiyo an sanya nasa take “Wata Makaranta Ta Fado Akan ɗalibai a karamar hukumar Toro dake jihar Bauchi.”

 Bidiyon mai tsawon dakika 58, wanda ya yi matuƙar daukar hankali mutane musamman a shafin Facebook, inda aka ga yara da dama suna ihu suna masu bada agaji na iya ƙoƙarin ciri yaran da suka makale a karkashin gini.

Tun daga wannan lokacin, bidiyon ya haifar da cec kauce inda kimanin mutane 139,000, suka tofa albarkacin bakinsu game da lamarin.

BINCIKE GAME DA LAMARIN

 Don tabbatar da lamarin, DUBAWA ta ƙaddamar da hotunan bidiyon zuwa bangaren nazarin inda ta yi amfani da Yandex da Google Reverse Image Search.  Inda Sakamakon ya nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar 13 ga watan Janairu, 2023, a lardin Sankuru, yankin Tsumbe, a Jamhuriyar Congo. Kuma ba a Yi asarar rai ko ɗaya ba, kimanin mutane 16 ne suka samu munanan raunuka. A lokacin an yi ƙoƙarin garzayawa da waɗanda abin ya shafa zuwa asibiti don duba lafiyar su

 GASKIYAR ZANCE

Gaskiyar magana shine wannan faifan bidiyo bashi da wata alaƙa da makarantun Bauchi, bincike ya nuna Ruftawar cikin ya faru ne a wata makaranta da ke lardin Sankuru, Tsumbe, Ƙasar Congo.

 Shaida ta biyu kum Yaren da aka yi magana da shi a wannan bidiyo ba Yaren ƙasa Najeriya ba ne bashida wata alaƙa da Garin Bauchi.

A binciken da Wikktimes ta yi ya gano cewar tabbas wannan lamari ya faru amma ba a Bauchi ba ,Lamarin ya faru ne a Ƙasar Congo.

 The researcher produced this fact-check per the DUBAWA 2024 Kwame Kari Kari Fellowship, in partnership with WikkiTimes, to facilitate the ethos of “truth” in journalism and enhance media literacy in the country.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories