NUJ Ta Karrama Mawallafin Jaridar Wikkitimes A Ƙoƙarin Sa Na Tsage Gaskia

Kungiyar ƴan jarida ta Najeriya (NUJ) ta karrama mawallafin WikkiTimes, Mallam Haruna Mohammed Salisu da lambar yabo ta shekarar 2024 wanda aka yiwa taken ƴancin ƴan jarida a yayin bikin ranar ƴancin ƴan jarida ta duniya.

 Mawallafin an bashi wannan karramawa ne bisa gagarumar gudunmawar da yake bayar wa wajen tsamo gaskiya, rikon amana, da shugabanci na gari a Arewa maso Gabashin Najeriya.

 Kungiyar ta NUJ ta jinjina wa Malam Haruna musamman ƙoƙarin da ya yi na fallasa cin hanci da rashawa duk da irin barazanar da yake fuskanta .Hukumar ta ba da misali da wani binciken ƙwaƙwaf da gidan jaridar ta Wikkitimes tayi a watan Janairun 2021 game da munanan ayyuka da ke gudana a wani asibiti da ƙasar Saudiyya ke ɗaukar nauyi wanda hakan ya haifar da yi masa barazana da kuma daukar matakin shari’a a kansa. 

Haka zalika a wannan shekarar ne jaridar WikkiTimes ta bayar da rahoton rashin gudanar da wani shiri na ilimi na Naira biliyan 1 da wani ɗan majalisar tarayya ya yi, wanda hakan ya sa aka gurfanar da shi a gaban kotu tare da cin sa tarar Naira biliyan biyu.

Bugu da kari, Mallam Mohammed ya taɓa fuskantar Shari’a a jihar Kano inda wakilin tarayya Abdullahi Sa’ad Abdulkadir ya gurfanar da shi kan labaran bincike daban-daban.

 Mawallafin ya fuskanci cin zarafi iri daban-daban; saboda akwai lokacin da  Hedikwatar ƴan sandan Bauchi ta tsare shi da kuma wani abokin aikin sa, tare da cin zarafinsa, biyo bayan rahoton da suka yi kan barazanar siyasa a yankin.

 An kuma kama shi tare da tsare shi a ranar zabe a watan Fabrairu saboda hira da mata masu zanga-zanga da ya yi. An yi hakan ne duk ɗan a tsorstar da Mohammed da tawagarsa.

 Duk da fuskantar kararraki takwas da ake ci gaba da yi, Mista Mohammed da tawagarsa a WikkiTimes na ci gaba da gudanar da aikinsu na bankaɗo gaskis tare da fallasa cin hanci da rashawa da kuma bayar da shawarar yin adalci.  Neman gaskiya da ya yi ba tare da ɓata lokaci ba ya sa ya sami karɓuwa da goyon baya daga cibiyoyin aikin jarida na duniya kamar Kwamitin Kare ‘Yan Jarida (CPJ), Cibiyar Binciken Aikin Jarida, (CCIJ),da sauran su.

Dr. Chris Isiguzo, shugaban NUJ na ƙasa a nasa jawabin ya ce an bayar da karramawar ne ga waɗanda ke kare ƴancin ‘yan jarida a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories