Ƙaƙaniƙayin Bashi Ya Sa Matashi Basajar Sake Shiga Musulunci

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Jihar Kano ta bayar da umarnin yi wa Haruna Abdulkarim mai shekaru 25 bulala goma don ladabtar da shi bisa laifin ƙaryar shiga musulunci.

Jami’an Hisbah yankin ƙaramar hukumar Kura su ne suka damko Abdulkarim.

 Rahotanni sun bayyana cewa Duk Juma’a ana ganin shi yana zuwa Masallaci a ƙoƙarin sa na ƙaryar ƙwadayin son shiga Musulunci, tare da neman taimakon sadaka sakamakon hakan da yake yi ya sa kwamandan Hisbah na karamar hukumar Kura Ali Alkasim ya ba da umarnin a kamo shi tare da mika shi ga yan sanda.

 Nan take aka gurfanar da shi a gaban kotu tare da tuhumar sa laifin da ake zargin ya aikata.

Bai musa ba ya amsa laifin sa tare da bayyana cewa tsananin bashi ne ya sa shi jefa kanshi cikin wannan hali. Sai dai ya roki a yi masa sassauci, inda ya sha alwashin ba zai sake irin wannan halin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories