Jos: An kama wani matashi daure da jigidar bama-bamai a harabar banki

Wata jarida mai kawo rahoto akan sha'anin tsaro a yankin tekun Chadi ta bayyana cewa an kama mutumin ne a garin Dadin Kowa dake karkashin karamar hukumar Jos ta kudu.

Jami’an tsaro sun kama wani matashi daure da sinadarai masu fashewa a cikin harabar wani banki dake Jos a jihar Filato.

Wata jarida mai kawo rahoto akan sha’anin tsaro a yankin tekun Chadi ta bayyana cewa an kama mutumin ne a garin Dadin Kowa dake karkashin karamar hukumar Jos ta kudu.

Jaridar mai suna Zagazola Makama ta bayyana cewa lamarin ya faru ne ranar Litinin, 13 ga watan Mayu.

A cewar jaridar, matashin ya yi shirin tayar da sinadaran ne a cikin harabar bankin kafin wani jajirtaccen jami’in tsaro a bankin ya gano shi.

Rahoton jaridar ya kara da cewa jama’a sun so daukar doka a hannunsu bayan an kama matashin amma aka lallashe su.

Jaridar ta kara da cewa ba zata ita iya tabbatar da cewa ko matashin yana da alaka da kingiyar ISWAP me tada kayar baya a yankin saharar Afrika ba.

KARANTA: Borno: Rundunar soji ta kama soja da alburusai da gurneti boye cikin buhun shinkafa

Jaridar ta ce yanzu haka matashin yana ofishin ‘yan sanda inda ake cigaba da gudanar da bincike.

Najeriya ta shafe fiye da shekaru 20 tana fama da aiyukan ta’addanci da suka hada da satar mutane domin neman kudin fansa, tayar da bama-bamai a wuraren taron jama’a da sauransu.

Wani rahoto da UNICEF ta wallafa a shekarar 2017 ya bayyana cewa an yi amfani da kananan yara 83 domin tayar da bama-bamai a iya cikin shekarar kawai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories