HISBAH ta kama matasa 20 maza da mata saboda yin wanka tare a Kano

Dakarun Hisbah, a karkashin ofireshon Kau da badala, sun samu nasarar kama matasan ne bayan mazauna yankin wurin shakatarwar sun shigar da korafi.

Dakarun rundunar Hisbah a Kano sun kama wasu matasa 20 a wani wurin shakatawa dake Ring Road a kwaryar birnin Kano.

Dakarun Hisbah, a karkashin ofireshon Kau da badala, sun samu nasarar kama matasan ne bayan mazauna yankin wurin shakatarwar sun shigar da korafi.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa babban mataimakin shugaban kwamandan Hisbah, Dakta Mujahidin Aminuddin Abubakar, ya ce laifin matasan ya sabawa dokokin Hisbah.

A cewar Dakta Mujahidin, dokar Hisbah ta haramtawa maza da mata cakuda tare domin yin wanka a cikin tafkin zamani.

KARANTA: Kano: Mutane uku sun rasa ransu sakamakon rikicin kauraye a wurin gangi

Da yake bayyana damuwarsa akan lamarin, Dakta Mujahidin ya ce matasan zasu iya amfani da kuruciyarsu da lokacin da suke batawa wajen yin wani abu da zai amfani rayuwarsu.

Kazalika, ya Kara da cewa za a hukunta matasan da zarar hukumar Hisbah ta kammala gudanar danbincike a kan lamarin.

Dakta Mujahidin ya yi kira ga iyaye da su saka Ido akan ‘ya’yansu tare da sanin wuraren da suke zuwa idan sun fita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories