Jerin sunayen manyan darektoci 14 da aka sallama daga aiki a CBN

A kalla ma’aikata 200 dake aiki a CBN aka sallama daga bakin aikinsu a ranar Juma’a, 24 ga watan Mayu.

Wannan sabuwar korar ma’aikata na zuwa ne bayan sallamar wasu ma’aikatan 117 da CBN ya yi a ranar 15 ga watan Afrilu da ya gabata.

Tun bawan zamansa gwamnan babban bankin Najeriya, Yemi Cardoso, ya shiga kaddamar da wasu tsare-tsare da suka hada da rage yawan ma’aikata.

Rahotanni sun bayyana cewa korar ta shafi manyan darektoci 14 daga cikin 17 da suka tsallake korar ma’aikata da babban bankin ya yi a watan Afrilu.

Manyan darektocin 14 sune kamar haka; 1. Clement Oluranti Buari 2. Dr Blaise Ijebor 3. Lydia Ifeanyichukwu Alfa 4. Jimoh Musa Itopa 5. Muhammad Abba 6. Rabiu Musa 7. Dr. Mahmud Hassan 8. Dr Ozoemena S. Nnaji 9. Dr. Omolara Duke 10. Chibuike D. Nwaegerue 11. Chibuzo A. Efobi 12. Haruna Bala Mustafa 13. Rakiya Shuaibu Mohammed 14. Benjamin Nnadi

KARANTA: Kano: Kotu ta daure ‘yan kasuwar canji 17 na tsawon wata shida

Tun a karon farko Cardoso ya sallami manyan darektoci da suka yi aiki tare da tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, wanda yanzu haka yake fuskantar tuhuma a gaban kotu.

Ko a yanzu haka, an fuskanci cewa korar ta fi shafar ma’aikatan CBN da ke aiki a karkashin ofishin gwamnan babban bankin, lamarin da wasu ke ganin cewa ba zai rasa nasaba da irin zargin badakalr da ake yi wa Emefiele ba.

Majiyarmu ta bayyana cewa korar ta shafi darektoci, mataimakan darektoci da masu biye da su a mukami, manyan manajoji da mataimakansu, da kuma wasu kananan ma’aikata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories