Mataimakin Gwamnan Kano Ya Ba Wa Nuhu Ribaɗu Haƙuri

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdulsalam, ya nemi gafarar Nuhu Ribadu, kan ikirarin da yayi na cewa Malam Ribadu ya taimakawa tsohon sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, wajen dawo Kano.

 Mataimakin Gwamna Abdulsalam ya ba da haƙurin ne a wani taron manema labarai da ya kira da yammacin Lahadi a gidan gwamnati dake Kano.

 In ba a manta ba dai a ƴan kwanakin baya ne aka ji Mataimakin gwamnan ya yi ikirarin cewa Malam Ribadu ya bayar da jiragen sama guda biyu domin taimakawa Aminu Ado Bayero dira garin Kano da ƙarfe 4:30 na safiyar ranar Asabar.

Wannan furuci na mataimakin Gwamnan ne ya tunzira Malam Nuhu Ribaɗu har ya yi iƙirarin ɗaukaka ƙara game da ƙazafin da aka yi mas.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories