Ku Gudu Ko Ku Mutu: ISWAP Ta Bawa Wasu Al’ummar Borno Notis

Kwanaki huɗu da kashe masunta goma sha biyar a yankin Tumbun Rogo,yanzu kuma ƴan ta’addar (ISWAP) sun sake Kunno Kai inda suka ba mazauna ƙaramar hukumar Kukawa sanarwar su bar yankinsu ko kuma su fuskanci kisan ƙare dangi.

Wani mazaunin garin da ya samu tserewq cikin garin Maiduguri sa’o’i uku da samun wannan barazana, shi ne ya bayyana hakan ga gidan talabijin na Channels.

 A yayin da ya ke ba da bayani ,mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa ƴan ta’addan sun tara jama’r dukkanin yankunan da sanyin safiyar jiya Alhamis, inda suka ba su umurni da su bar gidajensu kafin nan da ranar Asabar, in ba haka ba kuma su kashe su.

 A cewarsa, nan take jama’a suka fara barin yankunansu, wasu sun tafi Kross Kauwa yayin da wasu kuma suka nufi Monguno.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories