NAHCON Ta Ja Kunnen Mahajjata Kan Safarar Haramtattun Kaya Zuwa Ƙasa Mai Tsarki

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta gargaɗi maniyyatan Najeriya da su gujewa safarar haramtattun kaya irin su tabar sigari da goro zuwa ƙasar Saudiyya.

A cikin Wata sanarwa da mataimakiyar daraktar hulɗa da jama’a ta hukumar Fatima Sanda Usara, ta fitar a ranar Alhamis, ta bayyana cewa tafiya da haramtattun kayayyaki irin su goro da sigari zuwa ƙasar Saudi ka iya haifar wa mutum hukuncin kisa.

“Mahajjata su sani cewa a ƙasar Saudiyya ƙasa ce da ta kafu akan addini da al’adu, tana da tsauraran dokoki kan fataucin miyagun kwayoyi, wanda yin hakan hukuncin kisa ne. Saboda haka NAHCON tana tunatar da mahajjata cewa manufar tafiyar su Saudiyya don ibada ce, don haka kada su shagaltu da ayyukan da za su ɓata musu aikin Hajjin su,” cewar Daraktan hulɗar.

 Ta kuma gargadi alhazai da su sa ido su kiyayi wajen yin amfani da su a ɓoye haramtattun ƙwayoyin ba tare da sanin su ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories