Ƴar Gwagwarmaya Aisha Yesufu Ta Yi Biris Da Taken Najeriya A Wurin Taro

Aisha Yesufu, ƴar Gwagwarmaya mai fafutukar #BringBackOurGirls a wani faifan bidiyo da ta wallafa a shafin ta fito ƙarara ta nuna adawar ta ga sabuwar taken ƙasa da aka canza , inda aka hange ta ta yi biris taƙi miƙewa a lokacin da ake rerawa a wani taro da aka gayyace ta.

A wani faifan bidiyo da ta wallafa a shafinta na X a ranar Juma’a, 31 ga Mayu, Aisha Yesufu ta nuna ita sam ba ta goyon bayan wannan sabon taken da aka dawo da shi.

Inda take mai cewa ” Wannan take ba da Ni ba”

Bayyanar wannan bidiyo ya sa mutane da dama tofa albarkacin bakinsu inda wasu suke ganin cewar ko su ne haka za su yi,wasu kuwa gani suke hakan da ta yi ba abun burgewa ba ne.

In ba a Manta ba dai a cikin makon da ya gabata ne Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rattaɓa Hannu kan sake dawo da tsohuwar taken Najeriya da aka daina amfani da shi shekaru da dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories