Mafi Ƙarancin Albashi:Ƙungiyar Ƙwadigo Ta Tsinduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani

A yau ne Kungiyar ƙwadago ta tsunduma Yajin aikin gama gari kamar yadda ta ayyana biyo bayan rashin cimma matsaya tsakanin ta da gwamnatin tarayya game da  ƙarin N494,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

 Kungiyar dai ta nemi Gwamnatin tarayya da ta biya N494,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi tun a baya.

Buƙatar haka da ƙungiyar ta nema ya sa aka yi zama tsakanin shugaban majalisar dokokin ƙasar da ita kungiyar,wanda zaman ya shafe kimanin s’o’i uku jiya Lahadi a Abuja.

Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC, Joe Ajaero da takwaransa na Trade Union Congress (TUC), Festus Osifo su ne suka jagoranci sauran mambobin na kasa zuwa taron, wanda shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da kakakin majalisa Abbas Tajudeen suka jagoranta.

 Haka kuma Taron ya samu halartar sakataren gwamnatin tarayya, George Akume;  Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila;  Ministan Kudi, Wale Edun da Ministan Kasafi da Tsare-tsare na Kasa, Atiku Bagudu.

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron, Osifo ya ce duk da irin rokon da shugaban majalisar dattawan ya yi mana na mu yi haƙuri mu janye hakan bai samu ba dole Yajin aiki za a yi shi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories