Yanzu -Yanzu: Ƙungiyar Ƙwadago Ta Dakatar Da Yajin Aiki

Hadaddiyar kungiyar Kwadago (NLC) da takwararta ta TUC sun sanar da dakatar da yajin aiki na tsawon sati daya kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Dakatar da yajin aikin ya biyo bayan wata ganawa ta musamman da NLC da TUC suka gudanar da safiyar ranar Talata.

Bayan NLC ta rufe bankuna, makarantu, ofisoshin ma’aikatun gwamnati da sauransu, gwamnatin tarayya ta gayyace su domin tattaunawa a ofishin sakataren gwamnatin tarayya a daren ranar Litinin.

A karshen ganawar tasu, gwamnati da NLC sun cimma yarjejeniya akan mafi katrancin albashi wanda gwamnati ta bayyana cewa a shirye take ta biya fiye da N60,000 a wata.

An cimma yarjejeniya tsakanin NLC da sakataren gwamnatin tarayya George Akume a Abuja.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa bai kamata Musulmi su goyi bayan yajin aikin NLC ba – MURIC

Taron da ya samu halartar mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, inda ya nuna muhimmancin da gwamnatin Bola Tinubu ta ba wa wannan ɓangare.

 Duk da cewar dai ba a gama tsaida adadin abinda za a biya ba amma dai rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin tarayya ta amince za ta biya abinda ya fi N60,000 da ta ayyana zata bayar a baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories