Mafi Ƙarancin Albashi:Gwamnati Da Ƙungiyar Ƙwadago Sun Cimma Matsaya

Akwai yiwuwar kungiyoyin kwadago na NLC da TUC za su janye Yajin aikin da suka tsunduma a jiya Litinin sakamakon cimma matsaya da suka samu da gwamnatin tarayya kan sabon mafi ƙarancin albashi a ƙasar.

 An cimma yarjejeniyar ne a wani taro da sakataren gwamnatin tarayya George Akume ya kira a Abuja.  Taron da ya samu halartar mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, inda ya nuna muhimmancin da gwamnatin Bola Tinubu ta ba wa wannan ɓangare.

 Duk da cewar dai ba a gama tsaida adadin abinda za a biya ba amma dai rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin tarayya ta amince za ta biya abinda ya fi N60,000 da ta ayyana zata bayar a baya.

In ba a manta ba a jiya Litinin ne dai Ƙungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC suka fara yajin aikin sai baba-ta-gani  a ƙoƙarin su na tilastawa gwamnati amincewa da ƙarin albashin ma’aikata tare da duba karin da aka yi wa farashin wutar lantarki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories