Ranar Dimokiraɗiyya : Ba Zan Taɓa Juyawa Ƴan Najeriya Baya Ba – Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa ƴan Najeriya irin tallafin sa gare su inda ya yi alkawarin cewa duk rintsi ba zai taɓa yin watsi da su ba.

 Shugaba Tinubu ya yi wannan alƙawarin ne a yayin bikin zagayowar ranar dimokuradiyya ta ƙasa baki a yau Laraba.

 A yayin da yake jajanta irin matsalolin da tattalin arzikin kasar ke fuskan, Tinubu ya ce, “Na fahimci irin matsalolin tattalin arziki da muke fuskanta a matsayinmu na kasa. “Tattalin arzikinmu yana cikin tsananin bukatar gyara shekaru da yawa.  Babu daidaito a ɓangaren saboda an gina shi a kan kura-kuran dogaro da kuɗaden daga hakar man fetur.”

Haka kuma ya ƙara da cewa, duk da cewa ya san sakamakon sauye-sauyen da gwamnatinsa ta yi hakan ya kawo wahalhalu, amma suna kokarin ganin an gina ginshikin tattalin arziki mai karfi ga ƴan kasa.

Haka kuma shugaba Tinubu ya kara da cewa: “Ayyukan gyare-gyaren da muka bullo da su an yi su ne don samar da ingantaccen tushe mai inganci don ci gaban ƙasa duk da cewar mun sani gyare-gyaren sun haddasa wahalhalu ga ƴan ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories