‘Yan Majalisa Sun Bukaci FG Ta Gaggauta siyawa Tinubu da Shettima sabbin Jirage

Kwamitin tsaro a majalisar dokokin Najeriya ya bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta siyan sabon jirgin sama domin amfanin shugaban kasa, Bola Tinubu, da mataimakinsa, Kashim Shettima.

Hakan na kunse ne a cikin wani rahoto da kwamitin ya fitar bayan sauraron halin da jiragen saman shugaban kasa ke ciki ta fuskar amfani da su domin sufurin shugaban kasa da mataimakinsa.

“Wannan kwamitin yana da da ra’ayin cewa ya kamata a siyawa shugaban kasa da mataimakinsa sabon jirgi bayan gamsuwa cewa jiragen da suke amfani da su basu da koshin lafiya, a saboda haka ya kamata a gaggauta siyan karin sabbin jirage guda biyu domin tabbatar da tsaron shugabannin kasa,” a cewar rahoton kwamitin.

Rahoton, mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin, Honarabul Ahmed Satomi, ya kara da cewa siyen sabbin jiragen zai fi sauki a kan kudin da ake kashewa wajen kula da tsofin jirage guda shida da ke jibge, kowanne da matsalarsa.

‘Yan Najeriya sun sha yin korafi a kan yawan jiragen shugaban kasa wadanda ke lashe kudade masu yawa wajen kulawa da su.

KARANTA: Shettima, Tinubu da matarsa sun kashe N5.2bn a tafiye-tafiye, N12.5bn a kula da jirgi cikin wata uku

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya taba alkawarin cewa zai rage yawan jiragen ta hanyar siyar da wasu daga cikinsu amma hakan ba ta faru ba har ya sauka daga kan mulki.

Tuni kwamitin ya mika rahotonsa zuwa fadar shugaban kasa domin daukan mataki na gaba.

A ranar 23 ga watan Maris ne Honarabul Satomi ya fara gabatar da kudirin neman a sake siyan sabbin jiragen sama ga Tinubu da Shettima.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories